<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Zamanin da Almasihu Ɗan Allah LW592</title>
<lyrics>[V1]
 Zamanin da Almasihu Ɗan Allah
 Ya ji tausayinmu mu ɓatattu,
 Shi ma ya rabu da gida Ubansa
 Sa'annan ya zo zaman tare da mu.

[V2]
 KORUS
 Zuwan Mai Ceto ƙamna ta sa shi
 Allah ya ba shi don duniya duk
 Kada su halaka, sai dai su sami
 Ainihin rai irin nasa sosai.

[V3]
 2) Zaman Mai Ceto a cikin mutane
 Da yawan so da alheri ya ke
 Kowa ya nema ya gamu da Yesu
 Sani ya yi shi Mai Taimako ne.
 KORUS

[V4]
 3) Zaman nan nasa na bada alheri
 Aibunsa babu, bin Allah ya yi
 Ransa ya bayar don fansar mutane,
 Allah ya karɓa. Tsattsarka ne shi.
 Korus

[V5]
 4) Domin zunubinmu Yesu ya mutu,
 Bayan ya mutu ma sai biznewa
 Shi ma ya tashi a rana ta uku
 Sa'anna ya hau sama wurin Uban.
 Korus

[V6]
 5) Yesu Mai Cetonmu zai sake zuwa
 Daidai alkawali wanda ya yi
 Sa zuciyarmu dai kowace rana
 Yesu mu gan shi, mu gamu, mu ji.
 Korus</lyrics>
<hymn_number>592</hymn_number>
</song>